Lawan Ahmad ya yi bikin cika shekaru 14 da yin aure



Lawan Ahmad darakta kuma furodusa a masana'antar Kannywood ya cika shekara 14 da auren matarsa Saratu Abdulsalam tare da arzikin samun haihuwar yara hudu da Allah ya basu. 


A ranar Talata ne dai 25, ga Oktoba Lawan Ahmad ya wallafa hoton su shi da matarsa Saratu inda ya bayyana farin cikinsa da wannan tsawon shekaru da Allah yai musu na rayuwar aurensu. 


Yace tun da ya auri Saratu babu wani daga cikinsu da ya taba kai karar wani gidansu, sun zaune lafiya da juna babu wani sabani. Wannan ba karamin abin alfahari bane, inji shi. 


Don haka yana yiwa Allah godiya da irin wannan tsawon lokacin da suke zaune lafiya ba tare da an samu rabuwa ba. Kuma ina addu'ar Allah ya cigaba da bamu zaman lafiya ya Kara samana albarka, inji shi. 

.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post