Ina Cike Da Damuwa Kan Halin Da 'Yan Najeriya Suka Shiga - Inji Buhari


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari a cikin jawabinsa da yai na cika shekara 62 da Najeriya ta samu 'yancin kanta daga mulkin mallaka na Turawan Ingila. Ya yi wasu jawabi inda ya nuna damuwarsa da halin da ƙasar ke ciki.


Buhari ya fara jawabin ne da godiya ga ’yan Najeriya bisa hakurin da suka yi da kamun ludayin gwamnatinnsa a tsawon lokaci.


Buhari ya koka akan halin da 'yan Najeriya suke ciki inda ya ce abin tausayi ne. Domin abin na damuna sosai. Ina tabbatar muku da cewa hakurin ku ba zai tafi a banza ba.


Shugaban ya yi kira da jami'an gwamnati da malaman jami'o'i da su janye yajin aikin da aka ɗauki tsawon lokaci ana yinsa ba tare da an daidaita ba. Ya kara da cewa ya damu sosai kan jinkirin da aka samu a ɓangaren ilimi musamman rufe makarantu.


Don haka ina kira ga malaman jami'o'i da su yi hakuri su koma kan aikinsu kuma su ci gaba da tattaunawa da sauran bangarori da lamarin ya shafa don kawo karshen matsalar.


Sannan kuma shugaban kasa ya kara baiwa 'yan Najeriya hakuri akan matsalar rashin tsaro da ake fama da shi a sasan ƙasar. Inda yace gwamnatin su na ci gaba da yin kokari wajen karfafa hukumomin tsaro domin kawo karshen matsalar.


Buhari ya roki ’yan siyasa da jam’iyyu da su guji duk wani abu da zai kawo matsala ga zaben da za'a gudanar na 2023, domin a mika mulki ga gwamnati mai zuwa cikin kwanciyar hankali. Ya kuma yi kira ga mata da matasa da su shiga a dama da su sosai a zaben da ke tafe.


Ina fata matasanmu sun fahimci cewa tashin hankali babu abin da yake kawowa sai matsala ga zabe. Ina fata ba za su bari a yi amfani da su a wurin bangar siyasa ba a nan gaba,” in ji shi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post