HOTUNA: Jaruma A Cikin Shirin Kwana Casa’in Rayyya Ta Yi Bikin Kammala Karatunta


Fitacciyar jaruma a masana'antar Kannywood Surayya Aminu ta kammala karatunta Kamar yadda ta wallafa wasu Hotuna a shafinta na Instagram a makon da ya gabata. 


Surayya Aminu wacce akafi sani da Rayyya a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango da gidan talabijin na Arewa24 suke haskawa, ta nuna farin cikinta na kammala karatunta. 


Sai dai lamarin ya baiwa mutane mamaki sosai musamman masu sha'awar kallon fina-finan Hausa, wasu ba su yi tunanin cewa jarumar tana yin karatu ba, sun dauka cewa tunda tana harkar finafinai ba za ta samu lokacin zuwa makaranta ba. 


Jarumar dai ta yi wasu hotuna da abokan karatunta a ranar da suka kammala rubuta jarrabawar su ta karshe. Ita da abokan karatunta duk sun sanya fararen riguna wanda dalibai suka saba sakawa a ranar da suka kammala karatun su da ake "kira sign out". 


Wannan yasa mabiyanta a shafin instagram suka dinga yi mata addu'a da fatan alheri tare da taya ta murnar kammala karatunta. 


Ga hotunan da jarumar ta wallafa a shafin nata Kamar haka. 
















Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

5 Comments

  1. Ina mai tayata murna marar adadi Allah yasa alkairi yasa ya anfaneta duniya da lahira amma agskiya inasonta kuma da aure sai dai ni sojane kuma talaka nasan su sai Mai kudi suke aure amma nidai ina kaunarki kisani kikara sani see my number 09223516565 my name is muhammad Bello sarki

    ReplyDelete
    Replies
    1. Muna mana ftn Alkairi Allah yabaka ita

      Delete
  2. I don't mistake my number 09123516565 see my pic again

    ReplyDelete
  3. Congratulations in advance.
    May the acquired knowledge be beneficial to you and all the entire society at large 👌

    Amma wace school ta gama pls?

    ReplyDelete
  4. Masha Allah!
    Congratulations Rayyah may the knowledge and the certificate you acquired be bless and beneficial to you and the humanity at large.

    ReplyDelete
Previous Post Next Post