Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq; Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, sun yi jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Abdulganiyu Nuraini da mukarrabansa biyu da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da ta addabi jihar.
Shehin malamin wanda aka fi sani da Alfa Gani Aboto, da mataimakansa, Alfa Azeez Omoekun da Alfa Nurudeen, sun fito ne daga aikin da'awah a Minna, jihar Neja, a lokacin da ambaliyar ruwa ta tafi da motarsa kirar Toyota Yaris a lokacin da yake kokarin tsallaka gada kusa da Estate Harmony/ Kukende a unguwar Akerebiata dake Ilorin.
Hukumar kashe gobara ta jihar ce ta samo gawarwakin mutanen daga wani kogi daura da Olusola Saraki Abattoir dake kan hanyar Sobi Army Barrack, Ilorin a cikin motar ranar Asabar, 1 ga Oktoba, 2022.
Marigayi Sheik dalibi ne ga marigayi Sheikh Kamaldeen Al-Adabiy, Mufti na farko na Ilorin kuma ya kafa kungiyar Ansarul Islam Society of Nigeria. Sannan ya kasance hafeedh kuma babban mai koyar da haddar alqurani a jihar.
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka kai gawar tasa zuwa garinsu da ke Aboto a karamar hukumar Asa ta jihar bayan an yi janazar a Ilorin.
Gwamnan jihar a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa Rafiu Ajakaye ya fitar, ya bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da bakin ciki da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci da mataimakansa.
“Mun yi matukar kaduwa da alhinin rasuwar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Aboto da wasu ‘yan tsirarun wadanda har yanzu ba a san ko su waye ba, a matsayinmu na masu aminci, mun amince da hukuncin mahaliccinmu, muna rokon Allah Ya baiwa malamin da sauran wadanda abin ya shafa. Jannah Firdaus,” in ji Gwamnan a wata sanarwa.
“Wannan, hakika, labari ne mai ban tausayi da yawa. Rasuwar Sheikh Abdulganiy Aboto babban rashi ne ga al'ummar musulmi da ma Ilorin baki daya. Ya shahara da dimbin ilimi da kokari wajen yada sakonnin Musulunci cikin sauki ga masu sauraronsa”.
Allah Ya karbi Shahadarsu, Ya alarkanci bayansu
ReplyDeleteALLAH yasa sun huta
ReplyDelete