DOMIN SAMARI: Ku Guji Auren Mata Masu Irin Waɗannan Halayen Domin Samun Kwanciyar Hankalin Ku


Barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon rubutun wanda yana da matukar muhimmanci duk wani namiji musamman samari wanda ba su yi aure ba su sani. 


Maudu'in na yau ya kunshi nau'ikan mata guda shida da bai kamata ku aura a matsayin matan aure ba. Waɗannan halayen na iya haifar da karyewar gida nan gaba ko kuma su ba ku bakin ciki na tsawon rayuwa. 


Ga jerin nau'in matan da bai kamata ku aure su ba Kamar haka;


1.Ku guji auren macen da ta fifita kanta a kan ku, kuma ta fifita kanta a gaban kowa a rayuwarta. Ba za ta kasance daku ba a lokacin da kuke buƙatar ta ba.


2. Mai Son Abin Duniya (Materialistic/Money Freak)

Magana ta gaskiya babu wani ɗan adam da ba ya son abin duniya. Amma duk macen da kuka gane cewa tana son ku ne don abinda kuka mallaka ya kamata ku rabu da irin wannan matan. Duk macen da za ta dinga nuna muku tana son aje ayi shopping a siyo mata kaya ko kuma aje wajen sayar da abincin zamani aci dadi to ba macen aure bace.


3. Mai Yawan Yin Ƙarya

Ya kamata ku fahimci mace mai yin karya wacce duk tsarin rayuwar su a cikin karya suke. Auren irin wannan matan akwai matsala. Zamantakewar aure ba abune na wasa ba, da zarar kun fahimci wacce za ku aura tana da karya ku yi kokari ku rabu da ita.


4. Mai Cin Amana 

Ku guji yin rayuwa da macen da ba ta iya rike muku amana, irin wannan matan suna soyayya daku kuma suna soyayya da wasu mazan daban a bayan idon ku. Da zarar ka fahimci tana mu'amala da wasu mazan to rabu ita. Domin irin wannan matan ko kun aure su za su iya cin amanar ku a bayan idon ku, don haka ku guji yin mu'amala da irin su. 


5. Rashin Kulawa

Akwai matan da idan kana soyayya da su indai baka neme su ba su ba za su nemeka ba. Irin wannan matan ko shekara za ka yi baka neme su ba to su babu ruwan su kuma ba wai don basa sonka bane, a'a kawai rashin kulawa ne da rashin sanin muhimmanci soyayya.


6. Matan Da Basuda Kame Kansu

Duk macen da za ka same ta da tara kawaye to ba abokiyar rayuwa bace, wasu matan su gani suke birgewa ne tara kawaye wanda kuma hakan babbar matsala ce.


Ina fatan za ku yi nazari sosai akan wannan takaitaccen bayani akan nau'in mata shida da Bai kamata ku aura ba. ku bayyana mana ra'ayin ku a kasan wannan rubutun.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post