Jarumar finafinan Hausa Rukayya Umar Dawayya ta bude wani katafaren wajen gyaran jiki da kwalliya na mata a jihar Kano.
A ranar Laraba ne dai 26 ga Oktoba 2022 aka yi bikin taron buɗe wajen wanda akai masa suna da 'DY Utrat 85'. dimbin jama'a suka halarta, ciki har da manyan jarumai mata na masana'antar Kannywood duk sun halarta.
Katafaren wajen yana kan titin Guda Abdullahi dake a farm center cikin birnin Kano. A yayin bude wajen mahaifiyar jarumar itace ta yankan zaren bude wajen.
Tags:
Labaran Kannywood