An saka ranar daurin Auren Afakallah da jaruma Rukayya Umar Dawayya
Tsawon lokaci da aka shafe anata jita-jitar batun auren shugaban hukumar tace finafinai reshen jihar Kano Malam Isma'il Na'abba Afakalla da jaruma Rukayya Umar da akafi sani da Dawayya yazo ƙarshe domin kuwa an saka ranar daurin auren.
Ismail Na'abba Afakalla shine wanda ya wallafa katin gayyatar daurin auren a shafinsa na Instagram wanda za'a yi a ranar juma'a mai zuwa. Kuma Za a É—aura auren ne da Æ™arfe 2:00 na rana a ranar Juma’a, 4 ga Nuwamba, 2022 a Masallacin Juma’a na Tishama, dake Kano.
Tun tsawon watanni dai ake ta maganar batun auren nasu inda wasu ke ganin kamar ba dagaske bane wanda hakan yasa suka dinga karyatawa sai dai kuma tunda yanzu ta tabbata za'a yi wannan auren jama'a da dama sai yi musu addu'a suke yi da fatan alheri.
A satin da ya gabata ne jaruma Rukayya Dawayya ta buÉ—e wani katafaren wajen gyaran jiki da kwalliya wanda manyan jarumai suka halarci wajen domin tayata murna ciki har da ango Afakallah shima ya halarci wajen bikin buÉ—e wajen.
Ga katin dauren auren da ango Afakallah ya wallafa kamar haka.
Leave Comments
Post a Comment