Abin mamaki dai a duniya baya karewa, wannan yasa masu magana ke cewa idan kana da rai zaka ji kuma zaka sha kallo.
Wata mata 'yar asalin kasar Uganda mai suna Mariam Nabatanzi mai shekaru 40 ta haifi 'ya'ya 44. Daga cikin su guda 6 ne kawai suka mutu sauran 38 duk suna raye cikin koshin lafiya.
Babban dan shine mai shekaru 26 karamin kuma yana da shekaru 4. Mariam ta haife yaran nata su 44 da mijinta da ta aura tun tana budurwa.
Ta Haifi yara 'yan hudu sau 3 ta haifi yan uku sau hudu sai tagwaye('yan biyu) sau 6. Wanda a wasu lokutan akan samu mata masu irin hakan.
Tana da yanayin kwayoyin halitta wanda ke sa ta saki ƙwai da yawa wanda ke bata damar yawan samun daukar juna biyu mai dauke da' 'ya'ya.
Mariam Nabatanzi, Ana yi mata lakabi da Uwar Uganda. Wasu kuma na kiranta da uwar Afrika.