Labaran Ban Al'ajabi
AL'AJABI: Wani dan Najeriya ya auri mata tagwaye a rana daya
Monday, October 31, 2022
0
Wani dan Najeriya ya auri wasu ’yan uwa mata tagwaye a unguwar Ede da ke jihar Osun. Hotuna da faifan bidiyo sun karade shafukan sada zumunta.
Dan jarida, Sikiru Obarayese, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter, ya ce an daura aurensu ne a ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba.
Wata majiya ta gano cewa tagwayen sun auri mutumin ne saboda ‘ba za su iya rayuwa ba tare da juna ba’.
Kalli bidiyon yadda aka gudanar da daurin auren.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment