Abubuwa 2 wadanda maza ke yinsu da mata suka tsana


Maza suna yawan yin abubuwan da ke ɓatawa matan su rai. Maza, wannan darasin naku ne! Ku yi kokari ku gano wasu abubuwan da kuke aikatawa waɗanda matan ku basa so amma kuma su ba za su iya bayyana muku ba.


Ga wasu muhimman abubuwa biyu da ya kamata kusani da maza suke yi da yake ɓatawa mata rai.


1. Mazan Da Kwata-Kwata Basa Tambayar Mace Ko Nuna Damuwa Akan Halin Da Suke Ciki


Kai ba Chris Evans bane kuma ni ba Jimmy Fallon bane. Ina tsammanin hakan a bayyane yake, daidai ne? Don haka me yasa kuke nuna rashin damuwarku akan masoyan ku. Mata sun tsani namijin da ba ya tambayar halin da suke ciki.


Duk mace tana son kulawa daga wajen namiji wanda zai dinga nuna damuwarsa akan ta tare da nuna damuwarsa akan yanayin da ta ke ciki na rashin jindadi. 


Maza da dama ba su damu da su ji damuwar matan da suke zaune tare dasu ba. Hakan yasa matan suke kara shiga wani yanayi na rashin jindadi a rayuwarsu.


2. Rashin Nuna Soyayya

Duk mace tana so da burin ganin namijin da ta ke so ya damu da ita, sai dai maza da dama idan sun fuskanci mace na kaunar su sai su dinga yi musu wulakanci da girman kai, maimakon shima ya nuna mata kauna sosai amma sai ya nuna bai damu da ita ba .


Mace tana son kulawa sosai daga wajen namijin da ta ke so domin hakan yana kara saka mata nishadi da kwanciyar hankali a rayuwar ta. Amma indai ba za ta samu kulawa ba duk za ka samu ba ta da kuzari da annashuwa.


Da fatan maza za su Kula sosai wajen nuna soyayya ga matan su. Domin hakan zai kara kwantar mata da hankali da jindadin rayuwar ta.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

11 Comments

  1. Matan ne suma suna da tasu matsala wasu totally basu iya soyayya ba awajan miji

    ReplyDelete
  2. Munayi iya kokarinmu. Domin Muna koyi da annabi Muhammadu(S a w ). Shine kadai abin koyi

    ReplyDelete
  3. Allah ya samu. Gyara

    ReplyDelete
  4. Wai yaushe ne mata zasu godema Allah kan ni'imar da ya musu na azurtasu da maza kusa da su? Gskyn magana San kanku yayi yawa komai kune kuka iya kuma Ku kadae kukasan dadi ko? Mu duk abinda kuka man daidai ne kenan! Kai Allah ya iya mana da iyawanka

    ReplyDelete
  5. Wai mene yasa Maza su kebarin matansu a gida su Kuma su Tahoe legas su shape wata 8,10 aji tsoron Allah .

    ReplyDelete
  6. Assalamu Alaikum, couple lake of love and interest their not playing the roll in the marriage. While

    ReplyDelete
  7. Assalamu Alaikum, Am interested spinster (Budurwa) Wanda zanyi sure ko bazawara ga 08069641075 Whatsapp

    ReplyDelete
  8. Allah yasa muma mugyara

    ReplyDelete
  9. To Allah yasa mugane anma wani lokacin ne ku matan sai hakuri

    ReplyDelete
  10. Hmmm mata kenan
    Inada yarinya amma saboda taga inasonta sosai saigashi itace take min walukanci iya yadda takeso

    ReplyDelete
Previous Post Next Post