Yaran Da Basa Zuwa Makaranta A Najeriya Sun Haura Miliyan 20 - Cewar Rahoton UNESCO


Majalisar dinkin duniya ta koka game da yadda adadin yaran da ke daina zuwa makaranta ke karuwa, inda ta ce a yanzu adadin ya kai miliyan 244, inda kasashen India Najeria da Pakistan ke kan gaba wajen yawan adadin wanda basa zuwa makaranta. 


Ta cikin wani rahoto da hukumar kula da kananan yara ta Majalisar dinkin duniyar ta fitar, ta ce babban abin tashin hankali ne yadda adadin yaran da basa zuwa makaranta ke karuwa a kullum, duk da kokarin da ake tayi.


Hukumar ta UNESCO ta ce matsalar na kara girmama da bada tsoro a kasashen nahiyar Africa, inda Najeriya ke da yara sama da miliyan 20 da basa zuwa ko kuma suka daina zuwa makaranta, sai Itofiya da ke biye mata baya da adadin yara miliyan 10 da rabi, sai Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da ke da yara Miliyan 5 da dubu dari 9 sai kasar Kenya mai yara miliyan 1 da dubu dari 8.


UNESCO ta kara da cewa matsloli da dama na daga cikin dalilan da suka haddasawa yaran barin makaranta ciki kuwa har da tsananin talauci da ya kara kamari sakamakon barkewar annobar Corona, inda kuma aka ga bullar hakan har a kasashen da ba’a yi zata ba.


To amma duk da karuwar wannan matsala, hukumar ta ce batun fifita yara maza akan mata ta fannin zuwa makaranta ya ragu ainun a kasashen duniya musamman masu tasowa yayin da ya ragu da kaso 2 da rabi cikin dari na ‘yan firamare sannan ya ragu da kaso 3.9 ga daliban sakandare.


A Najeriya dai adadin yaran da basa zuwa makaranta kullum karuwa yake yi musamman a arewacin kasar wanda ake danganta yankin da yawan al'umma da kuma talauci. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post