Gwamnatin tarayyar ta sanar da dakatar da shirin ta na karin kudin harajin kiran waya. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Pantami ne ya sanar da dakatarwar a yau Litinin.
Ya sanar da hakan ne a yayin taron kaddamar da kwamitin shugaban kasa haraji kan hanyoyin sadarwa don bunkasa bangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja.
Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa.
Gwamnatin tarayya ta hannun ofishin kasafin kudi na tarayya a baya ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da shirin fitar da kudaden da ta ke bukata a kan harkokin sadarwa da abubuwan sha a shekarar 2023.
Sai dai Pantami ya ci gaba da cewa ba ya goyon bayan aiwatar da wannan harajin da zai kara tsadar harkokin sadarwa ga ‘yan Najeriya.
Idan ba'a manta ba tun a watan da ya gabata ne aka tabbatarwa da yan Najeriya cewa za'a fara gudanar da tsarin karin haraji a duk kiran waya da kuma sayen data.