Yanzu muke samun rasuwar Malam Umar Yahaya Manunfashi rasuwa bayan fama danna rashin lafiya wanda ya shafe makonni a wani asibiti sake Kano.
Falalu Dorayi shine wanda ya sanar da hakan rasuwar jarumin a shafinsa na Facebook inda yai rubutu Kamar haka:
"INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJI'UN!
Allah yai maka rahma Baba Umar
(Bankaura/Kafi Gwamna)
Umar Yahaya Mununfashi na daya daga cikin Iyaye Jarumai da suke bada muhimmiyar gudunmawa a Masana’antar Kannywood. Tun daga Stage Drama zuwa Television har Home Video (Kannywood) Sannan Babban Ma’aikaci ne A Nigerian Customs Service.
Allah Yai masa gafara ya bawa iyaye da iyalai da Yan uwa hakurin rashinsa. Idan mutuwar tazo Allah kasa mu cika da imani.
Amin."