Christopher Musa wanda shine Shugaban Operation Hadin Kai a arewa maso gabashin Najeriya yace akalla 'yan ta'adda dubu 80 ne suka mika wuya ga rundunar Sojin Najeriya.
Musa ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a birnin Maiduguri a wata tattaunawa da yai da manema labarai kan nasarorin da rundunar ke samu a baya-bayan nan.
Kwamandan ya ce ci gaba da kai hare-haren da ake kai wa 'yan tada kayar baya su ka mika wuya.
A cewarsa, hakan ya sa a ka bukaci a samu karin sansanoni a Maiduguri domin karbar tubabbun da aka ware domin tantance maharan da wadanda ba mayakan ba.
Ya yaba da goyon bayan da jama’a ke ba su, wanda ya bayyana a matsayin “jarumai ” ya kuma bukace su da su ci gaba da dagewa wajen ganin an kawo karshen rikicin cikin gaggawa.
Muna matukar farin ciki da yadda jama’a ke ba mu hadin kai; suna ganin ikhlasi a cikin abin da muke yi.
Mun himmatu wajen bin ka’idojin kare hakkin dan Adam da ka’idojin tafiyar da ayyukanmu,” in ji Musa.
A baya-bayan nan daina tawagar sojin Najeriya da hadin gwiwar operation hadin kai suna samun galaba a gumurzun da suke yi da 'yan bindiga.