Yadda Za Ku Ragewa Wayar Ku Shan Data Cikin Sauki


Yawan data da ake amfani da ita da kuma kudin da ake siyan data ya yi yawa, haka kuma data ba ta daukar lokaci take karewa. Da zarar ka fara amfani da ita sai ta kare.


A kullum za kaji mutane da dama suna korafin cewa data da suke yin amfani da ita wajen bude kafofin intanet ba ta yi musu auki da zarar sun fara yin amfani data sai ta yi saurin karewa.


Wasu har suna daura laifin ga kamfanonin da suke sayan data. Sai dai kuma a wani bincike Da na gudanar na gano cewar yawan shan data da mutane suke korafi ba laifin kamfanonin layin ku bane.


Akwai abubuwa da dama a kan wayoyin ku da suke sha muku data da baku sani ba. Shi yasa muka kawo muku abubuwan da suke saurin shanye muku data da kuma yadda za ku tsayar da su.


Duk da haka, akwai shawarwari da ya kamata ku gwada yin amfani dasu don dakatar da yawan gudun shan data a wayoyin ku.


1. Ku Kunna Wajen Data Na Kan Wayar Ku (data saver mode) 

Kowace waya (smartphone) tana da wannan fasalin. Abin da kawai za ku yi shi ne kuje zuwa ‘Settings,’ sai ku danna kan data wayar ku. Wannan zai taimaka muku wajen tsayar da tallace-tallace da suke shigowa wayar ku da zarar kun bude data. 


2. Ku Rage Adadin Shafukan Da Suke Amfani Da Data Na Bayan Fage (background data use) 

Background data shine wasu manhajoji (applications) da ba ku yi amfani dasu ba amma kuma a boye ta bayan fage suna amfani da data. Manhaja(apps) suna da jan data wajen kawo talla a wayar ku da sabunta manhajojin wayar ku. 

Don rage yawan shan data a wayoyin ku, hanya mafi sauki shine ku dakatar da manhaja(app) da suke aiki a bayan fage (background data) 


Don samun damar wannan akan wayoyin iOS: Danna "Settings" 

Danna "General" 

Nemo "Background App Refresh" Sannan danna "off" 

Akan wayoyin Android: 

Je zuwa "Settings" 

Danna kan "Connections" ko "Mobile networks" 

Danna "Amfani Data" 

Danna "amfani da bayanan wayar hannu" 


3. Rage Amfani Da Soshiyal Midiya (Social Media) 

Amfani da soshiyal Midiya na daya daga cikin abubuwan dake Kara yawan shan data a waya. Domin rage shan data a wayoyin ku sai ku rage yawan shiga shafukan soshiyal midiya. 


4. Rage Amfani Da Data Akan WhatsApp

Automatic download na cikin WhatsApp na taimakawa wajen shan data da yawa a wayoyin ku, yana da kyau ku Kashe automatic download na kan WhatsApp din ku. Hakan zai taimaka muku wajen rage shan data. 

Je zuwa "WhatsApp" 

Danna "Settings" 

Danna "Storage da Data"

Danna kan “media auto-download” ku tsayar da media auto download.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post