Rundunar 'yan sandan jihar Kano Kano sun kake wani dan kasar China mai suna Mr Geng kana zargin sa da kashe wata tsohuwar budurwarsa Ummukulsum Buhari a unguwar Janbulo.
Tun da farko dai ance shi Mr Geng da Ummukulsum Buhari sun yi soyayya a baya tun kafin tayi aure, amma daga bisani ya sami labarin tayi aure (kamar yadda ya fada).
A hirar da Feedom Radio ta yi da wani makusancin Ummita ya bayyana cewa marigayiyar sun shafe kusan shekaru biyu suna soyayya ita da Mr Geng kafin tayi aure da wani.
Dan haka yayi fushi yaje gidan ta ya haura ta taga ya kashe ta a unguwar su dake Janbulo, wanda daga baya aka kaita asibitin UMC anan ta rasu.
Ummukulsum ne sunan ta amma an fi kiran ta da Ummita, ta gama digiri a fannin aikin gona daga jami’ar Kampala dake Uganda yanzu haka tana bautar kasa a Sokoto.
Jami’an immigration da yansanda ne suka kwace shi daga mutanen da suka fara dukansa a yankin Jan bulo kusa da layin Lawan Kyankyan, yanzu haka dai yana hannun 'yan sanda.