Yadda Wani Boka Ya Ɗirkawa Wata Matar Aure Ciki a Jihar Bauchi Bayan ta Kai 'Yarta Ayimata Magani


A yanzu haka wani boka ya zabgawa wata matar aure ciki a jihar Bauchi dake Arewa Maso Gabashin Najeriya. 


Bokan ya yi wa wannan matar aure ciki ne a lokacin da ta kai 'yar ta domin a yimata magani.


Tuni dai 'yan sandan jihar ta Bauchi su ka kama wannan boka domin girbar abin da ya shuka.


Kakakin rundunar 'yan sandan jihar a jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce wanda ake zargin mai kimanin shekara 32 na karamar hukumar Tafawa Balewa, ya yi amfani da kayan maye ne wajen gusar da hankalinta kafin ya yi mata fyaden kamar yadda kamfanin dillacin labarai (NAN) ya wallafa.


Wakil ya kuma ce sun kama wani malamin makaranta mai kimanin shekara 25 da ake zargi da yi wa dalibarsa mai shekara bakwai fyade a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.


Ya ce, “Bayanan da ’yan sanda suka tattara sun nuna cewa wanda ake zargin, mazaunin unguwar Ajiya a garin na Alkaleri, malami ne a wata makaranta mai zaman kanta a garin.


“Jamia’nmu sun kuma kama wani mai sayar da askirin a garin Bauchi, saboda zargin yin luwadi ga wani yaro mai shekara 12 a bayan wani banki a Alkaleri.


“Binciken farko-farko ya nuna wanda ake zargin ya sayi ruwan leda ne daga hannun yaron, sannan ya yaudare shi zuwa cikin wani shago ya yi lalatar da shi a ciki,” inji Kakakin ’yan sandan.


Daga Suraj Na'iya Kududdufawa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post