Wasu Wurare 8 Da Zaka Tabawa Matarka Su Ka Zunguro Mata Sha'awa Da Soyayyar Ka



A wannan rubutun za ku ji wasu muhimman abubuwa da suke Kara zafin soyayya tsakanin miji da mata wanda ya kamata duk wani mai aure yasani. 


Ba sai da kalamai kadai kake iya tsokano soyayyar matarka ba. Akwai wasu muhimman Wurare da mata suke son mazajensu su rika yi musu wasa da wajen. 


Nasan ba kowane magidanci ne yasan hakan ba, shiyasa muka shirya sanar daku yadda ake yi domin ku Kara samun soyayya tsakanin ku da matan ku. 


Ga jerin abubuwan kamar haka:


1: Akasarin mata suna son mazansu su tabamusu kafadansu.

Mace tana so idan tana zaune ka tsaya a bayanta kana matsamata kafadanta kaman yi mata tausa.

Ka kula a wannan lokacin ko hira take yi sai ta sauya sauti, saboda yadda wannan wasan yake shiganta yana kaimata wani sako na ratsa jiki. 


2: Idan kana zaune da matarka ka tallafota kana wasa da kunnunwanta. Nan take zata dauke wuta.

Akwai nau'ukan wasa da kunnuwan mace kusan kashi 3 da

mata suke matukar so da kauna, ka yi kokarin yi mata su.


3: Mata suna son ka daura dan yatsanka ka rufe mata bakinta.

Sai ka sunkuya ka yi mata rada da wani kalmar soyayya a kunnunwanta.

Wayyo idan ka samu macen da ake cewa romantic ba zaka daga kanka sama ba sai ta hauka da tsotso baki(kiss). 


4: Kasan cibiyar duk wata mace wurine da take son ji mijinta ya taba mata shi.

Bama wai tabawa kawai ba ka shafa mata wajen.

Misali idan ka rungumota ta baya, sai ka sa hannunka kasan cibiyanta zuwa maranta kana shafamata shi.

Wannan salon soyayyar yana kidimar da mata musamman idan auren soyayya akayi.


5: Mata suna son idan suna zaune ka dauki kafafuwanta ka daura akan cinyoyinka kana matsa mata tafukan kafafuwanta kana

mata tausa a hankali kana jan yatsunta cikin soyayya.


Kadan kenan daga cikin abubuwan da mace ke bukatar mijinta ya Rukayya yimata kenan wanda ke Kara mata soyayyar ka a zuciyar ta. Sai dai wasu mazan sun san hakan amma saboda girman kai ba za su yi ba. 


Daga yau din nan ka gwada yiwa matarka wasa da wadannan wuraren kasha mamaki. Da fatan kun amfana da wannan takaitaccen bayani. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post