Wasu Muhimman Hanyoyin Nasara A Rayuwa 15 Da Ya Kamata Ku Sani


A wannan rubutun da matashi mai ilimin kwamfuta yai Mohiddeen, za kuji wasu muhimman hanyoyin na samun nasara a rayuwa da ya kamata kowa yasani. 


1. Ka so abun da kake yi, wato ka samu passion, saboda fadin Jeff Bezos cewa "love what you do" 


2. Ka gina kudiri a rayuwarka sannan ka san mene ne dalilin yin wannan abun da za ka yi


3. Ka saita tunaninka bisa kyakkyawan tsari mai nagarta, ba tunanin faduwa ko sarewa ba


4. Ka farka daga dogon baccin da kake yi ta hanyar karance-karance da bincike


5. Ka yarda da kanka, ka yi hakuri, ka jajirce sannan ka yi aiki tukuru


6. Ka fara a hankali da kadan-kadan, kada ka dauko dogon buri ko kwatancen kanka da wasu


7. Ka san wane mataki kake son zuwa kuma ta yaya za ka je. V cewa ya yi idan ba ka san inda za ka je ba akwai matsala


8. Ka samu wani ya rike hannunka, wato maigida ko kuma wani wanda kake koyi da shi don ya rinka ba ka shawara da saita ka a kan hanya


9. Ka yi kokari ka ba da himma a kan wani al'amari na musamman, idan ka ga alamar matsala ka canja taku


10. Ka shirya karban suka da kalubalai daga wajen mutane, sannan ka yi admitting cewa za ka iya faduwa saboda ko da ka fadi za ka sake tashi nan take don ka sake gwabzawa


11. Ka san ta yaya za ka rinka amfani da lokacinka cikin hikima da azanci


12. Kada kullum ka yi kokarin zama perfect, kowanne jarumi sai da ya gwabza kuma a karo a farko an kada shi, sannan an ce sai da koyo ake dacewa


13. Duk abun da za ka yi ka tabbatar ka yi bincike a kai da dogon nazari sannan kuma da hikima


14. Ka rinka yin kididdiga da kiyasi a al'amuranka, sannan ka kalli gabanka kai-tsaye zuwa kudirinka wato matakin da kake son kai wa


15. Ka yi aiki na gari


Da Fatan matasa za ku yi amfani da wadannan muhimman hanyoyin da muka bayyana muku domin cimma nasara a rayuwar ku. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post