Fitaccen jarumi a masana'antar Kannywood Tijjani Faraga ya bayyana cewa ba za su ragawa dukkan masu sukar finafinan Hausa da bata musu suna ba, domin kuwa akwai tarin masu ilimi sosai a masana’antar.
Duk wadanda ke neman bata mana suna ba za mu kyaleshi ba ko wanene, domin muma mutane ne Kamar kowa kuma muna da dang da 'yan uwa da iyali, don haka ba za mu zuba ido kowane banza da wofi yana cin mutuncin' 'yan film ba.
Domin film itace sana'ar mu, ta yimana riga da wando da ita muke ci kuma muke sha. Kuma babu wanda muke zagi, don haka ba za mu iya zuba ido ana cin zarafin mu ba domin muma muna da 'yanci kuma muma 'yan kasa ne.
Faraga ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya aikewa shafin jaridar Film Magazine. Inda ya Kara da cewa idan muna yin wani abu wanda ba daidai ba kamata yai ku kira mu ku sanar damu domin mu gyara. Amma ba za mu bari a bayan fage ana zaginmu da aibata mu ba.
Sai dai daga bisani wakilin Film Magazine ya tuntubi Tijjani Faraga kan dalilin da yasa yake yin wannan maganganun inda ya bayyana musu cewa.
Abin da ke faruwa, ai kun ji labarin wanda ya ke maganganu barkatai a kan ‘yan film, wanda Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya kai shi kotu. Kishin abin ne wallahi ya sa na yi wannan rubutun, kuma na ke ja wa jama’a kunne lallai su san cewa mu ma mu na da masu ilimi wadanda idan su ka yi mana abu ba za mu iya bari ba.
Ka ga dai abin da Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya yi abu ne da ake ce wa ‘eye opener’. Da ma duk abin mun yi shiru ne ana kallon mutane ana jin irin abubuwan da su ke fada. Kuma mu a harkar tamu akwai abin da mun yi shi ne saboda mu nemi mafita a rayuwar mu, ma’ana ta kasance sana’a a gare mu, ta kasance gatan mu, ta kasance a kowane lokaci ita mu ka sani, ba mu yin wani abu.