Rundunar Sojin Najeriya Sun Yi Nasarar Hallaka Manyan Kwamandojin Mayakan ISWAP


Wani gagarumin hari da rundunar Sojin Najeriya ta kai a maboyar mayakan ISWAP sun yi nasarar kashe manyan kwamandojin 'yan ta'addan ISWAP tare mayakan su daga bangarori da dama na dajin Sambisa. 


Wata majiyar leken asiri ta tsaro ta shaidawa PRNigeria cewa, dakarun da ke karkashin Operation Hadin Kai, sun kaddamar da hare-haren ba zato ba tsammani daga bangarori daban-daban a gefen dajin Sambisa.


“Rundunar sojin Najeriya ce ta kaddamar da farmakin bayan da wasu bayanan sirri suka bayar da takamaiman wuraren da kwamandojin ‘yan ta’addan da sojojin da ke kafar su suke.


“Kafin a fara aikin, rundunar sojin sama ta tura manyan jiragen yaki da kuma Super Tucano domin samar da hanya ga sojin kasa.


“Dakarun kasa sun yi nasarar harba rokoki da aka auna kan maboyar kwamandojin da mayakansu.


Ko a ranar Asabar ma rundunar sojin Najeriya tare da hadin gwiwar Operation Hadin Kai sun kai wani mummunan hari ga maboyar Boko Haram dake karamar hukumar Bama inda suka kashe da dama daga cikin mayakan yayin da wasu kuma suka nutse a cikin kogi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post