Rasuwar Umar Bankaura Babban Rashi Ne Ga Masana’antar Kannywood Wanda Zai Yi Wuyar Cikewa - Inji Bello Ja


Alhaji Isa Bello Ja wanda fitaccen dan film ne da aka yi shekaru ana damawa dasu, ya bayyana rasuwar Umar Yahaya Malumfashi a matsayin babban rashi a masana'antar Kannywood wanda zai yi wuya a samu maye gurbin sa a cikin karamin lokaci. 


Bello Ja ya bayyana cewa mutuwar Bankaura ta shafi kowa da kowa musamman wanda suke harkar finafinan Kannywood duba da irin gudunmuwar da ya dade yana bayarwa a masana'antar Kannywood tsawon shekaru. 


Ya Kara da cewa Umar Bankaura mutumin kirki ne kuma mai ibada domin shi mutum ne da baya yin wasa da addini. Duk inda ya samu kansa lokacin sallah ba ya yin wasa. Kuma kowa ana cikin yin aiki idanun lokacin ibada yayi sai ya ba da umarnin aje ayi sallah. 


Ni da shi Kamar 'yan uwa muke, aminina ne sosai kuma iyalina da nasa mun hada su suna  yin zumunci. Mun dade sosai a harkar Film tun tsawon shekaru da suka wuce kuma ba mu taba samun wani kalubale tsakanin mu ba. 


Don haka babu abinda za mu ce sai dai mu yi masa addu'a da fatan Allah ya jikansa, Allah ya kyauta makwancin sa, su kuma iyalinsa Allah ya albarkace su ya raya su cikin aminci, inji Bello Ja a wata hira da yai da Mujallar Film Magazine. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post