Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta ja kunnen al'umma Najeriya musamman wanda suke yin amfani da kayayyakin kwalliya don canja launin fatar su.
Hukumar ta ce duk masu yin amfani da irin wannan kayan domin sauya launin fatar su daga baki zuwa fari da su daina. Hukumar ta bayyana cewa irin wannan kayan da ake amfani dasu don sauya launin fata suna da illa ga lafiya.
NAFDAC din ta sanar da hakan ne ta hannun mai magana da yawun ta Olusayo Akintola wanda ya sanarwa da manema labarai a ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce za su kama duk masu tallata irin wannan sinadaran domin hukunta su. Inda ta ce kayan an harmata sayar dasu da kuma yin amfani dasu a fadin kasar bakida daya domin sinadaran suna da lahani ga jikin dan adam.