Kowace mace tana da irin abubuwan da take sakawa a jakarta a yayin fita daga gida domin zuwa unguwa, wajen aiki Ko makaranta wanda sukayi hada da kayan kwalliya wayar salulua caja da sauran su.
Kamar yadda wadannan abubuwan suke da muhimmanci a cikin jakar ki, akwai wasu muhimman abubuwan da ya kamata ace kina dauke dasu a cikin jakar ki koda yaushe.
Kowa yana da nasa jeri na musamman a kan lokacin da ake yin safa da kayan masarufi, gami da pads na tsafta, lipstick, bankin wuta, caja, da sauransu. Kamar yadda mahimmancin waɗannan abubuwan ke da su a cikin jakar ku, akwai ƴan manyan abubuwa waɗanda ke da mahimmanci a samu a cikin jakar ku ta yau da kullun.
1.Tishu (kyalle)
A lokacin da kike tafiya cikin rana, ba zaki San lokacin da zaki bukaci amfani da tishu ba, hakan zai sa ki bukace shi saboda zafin rana wanda kan iya haifar miki da gumi. Don haka yana da matukar muhimmanci a duk lokacin da zaki fita ki tabbatar kin saka kyallen tishu a jakar ki.
2. Minti (Alewa)
A duk lokacin da kika tattara abubuwan da zaki zuba a cikin jakarki ki tabbatar kin hada da alewa, domin wani lokacin zaki iya ci Ko shan wani abu da kan iya canja miki dandanon baki, misali kamar sha Ko cin abin da ya danganci tafarnuwa Ko albasa wanda hakan zai iya sa bakin ya dinga warin su.
Yin amfani da alawar minti kan iya kare ki daga wannan warin. Don haka kada ki manta da saka alawar minti a cikin jakarki a koda yaushe.
3. Turare
Wani lokacin Ina mamaki idan na duba jakar mace babu turare a ciki, hakan babban Kuskure ne. Domin a lokacin da kika shafa turare a jikinki idan zaki fita zai iya bin iska a dalilin yin zufa wanda hakan kan iya canja kamshin jikinki.
Amma idan kinaso da turare a cikin jakarki ba zaki samu wannan matsalar ba. Don haka ki tabbatar a koda yaushe kina dauke da turare mai kamshi a cikin jakarki, hakan zai taimaka miki ki kasance cikin kama hi a koda yaushe.
4. Man Lebe (Lip Balm)
Kasancewa da man lebe a tare dake abunw mai matukar muhimmanci, domin shi lebe musamman na mace idan yana bushe babu Kyaun gani. Idan an saka man lebe baya daukan dogon lokaci yake bushewa.
Yana da muhimmanci kada ki manta da man lebe a cikin jakarki a duk lokacin da zaki fita daga gida.
5. Pampas
Idan mace tana da jariri, yana da matukar muhimmanci ta tanadi pampas a cikin Jakarta. Ana so a dinga yawan canja pampas ga yaro. Abin mamaki wasu matan sai su saka pampas ga jaririn su yai sama da awanni biyar a jikinsa. Yin hakan Kuskure ne kuma ya kan iya jawo wata matsala ga yaron.
Wannan sune wasu daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata duk mace ta dinga tafiya dasu a cikin Jakarta domin kare kanta daga fadawa matsalar warin jiki, zufa da datti.