Mayakan Boko Haram sun kashe masunta a yankin Tafkin Chadi sun yi awon gaba da wasu da dama, yayin wani farmaki da suka kai yankin tafkin Chadi da ke jamhuriyar Nijar, a cewar wata majiyar tsaro.
Arewa maso gabashin Najeriya dai na fuskantar rikicin mayakan jihadi na tsawon shekaru 13 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba wasu kusan miliyan biyu da muhallansu tun daga shekarar 2009.
Kisan masuntan a wannan makon na nuna yadda rikici ya kunno kai a kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da ke makwabtaka da kasar, musamman a tsibiran tafkin Chadi da ke da dabarun yaki inda mayakan jihadi suka kafa sansanoni na boye.
Mayakan sun yiwa masunta da dama kawanya a tsibirin Kwatar Kaoulaha da ke yankin Diffa a ranar Lahadi zuwa litinin, inda suka kashe wasu tare da yin garkuwa da wasu saboda rashin bin umarnin da aka ba su na barin yankin, kamar yadda wasu masunta suka shaida wa AFP.
“Masunta da dama ne mayakan Boko Haram masu biyayya ga Baakura Buduma suka kashe tare da yin garkuwa da wasu saboda rashin barin yankin kamar yadda aka umarce su,” inji Kallah Sani, yayin da yake bayani kan wani shugaban kungiyar Boko Haram na yankin.
Sani bai iya bayar da takamaimai adadin ba amma ya ce wadanda suka tsere sun shaida masa masunta da dama suna tsibirin a lokacin da aka kai harin.
Mutumin dai na daga cikin masunta kusan 300 da suka yi biyayya ga sanarwar barin aiki na sa’a guda, inda suka bar aikin da sauran dukiyoyinsu ga mayakan jihadi..
"Sun gaya mana cewa za su kwashe duk abin da muka mallaka a matsayin ganima tunda gwamnatinmu ta kwace musu kudadensu," kamar yadda ya shaida wa AFP.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne kungiyar Boko Haram ta umarci masuntan wadanda galibinsu ‘yan Arewa maso yammacin Najeriya ne da su fice daga yankin tare da barin dukiyoyinsu a matsayin ganima ga mayakan, inji wani masuntci, Anas Ibrahim.
“Masu tayar da kayar bayan sun dawo ne a ranar Lahadin da ta gabata inda suka kashe wadanda suka samu tare da lalata kwale-kwalen su na kamun kifi don hana su tserewa,” inji shi.
Mayakan Boko Haram dai a baya-bayan nan sun addabi yankin tafkin Chadi inda suke yawan kai hare-hare wanda ke sanadin asarar rayuka tare da lalata dukiyoyi. Sai dai haryanzu mahukunta sun kasa daukar Matakan da suka dace wajen dakile ayyukan 'yan tada kayar baya.