Wasu hotuna da suke yawo a shafin soshiyal media musamman a kafar sadarwa na instagram anga hotunan da ake yi kafin aure da ake kira da "pre-wedding pictures" na Mawaki Ado Gwanja da Mome Gombe.
Tun da farko dai Ado Gwanja ne ya fara wallafa hotunan a shafinsa na Instagram inda a kasan hotunan ya rubuta "Masha Allah". Wanda jama'a da dama suka dinga fatan alheri daga ciki har da babban jarumi Ali Nuhu.
Daga bisani itama Mome Gombe ta wallafa hotunan a shafinta inda itama ta rubuta "masha Allah". Hakan yasa ake tunanin cewa za su yi aure ne duk da babu wata sanarwa daga bakin su.
Shi dai Ado Gwanja ya rabu da matarsa tun a bara wanda kuma a yanzu haka bashida aure, hakan yasa ake tunanin ki zai yi wuff da Mome Gombe.