Labaran Kannywood
Jarumar Kannywood Bilkisu Abdullahi Ta Sayi Sabuwar Mota Ta Miyalan Hamsin
Friday, September 9, 2022
0
Fitacciyar jaruma a masana'antar Kannywood Bilkisu Abdullahi ta sayi sabuwar mota wacce kudinta ya kai miliyan 50.
Jarumar ta wallafa hotunan motar ne a shafinta na Instagram, inda ta dauki hotunan tare da motar cikin murna da nuna farin ciki.
Jarumai mata a masana'antar Kannywood a wannan lokutan ana yawan ganin su tare da manyan gidaje da motocin alfarma wanda ba Kasafai aka saba ganin irin hakan a shekarun baya ba.
Ko a baya-bayan nan ma wasu hotuna sun dinga yawo a kafafen sada zumunta inda itama Nafisa Abdullahi aka ganta da wata mota ta alfarma wacce aka bayyana kudinta yakai miliyan 30.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment