Jami'an Tsaro Sun Kubutar Da Mutane Bakwai Wanda 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su A Kaduna


Jami'an tsaro sun yi nasarar kubutar da wata mata da 'ya'yanta uku tare da wasu mutumina uku wanda yan bindiga suka yi garkuwa dasu a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna. 


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa an kubutar da mutanen ne a yayin wani sintiri da jami'an tsaro na Operation Forest Sanity suka kai a yankin na Birnin Gwari inda suka yi nasarar kubutar da mutanen da 'yan bindiga suka sace. 


Mr Samuel Aruwan wanda shine Kwamishinan tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna shine ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook. 


Inda ya bayyana cewa gwamnatin Kaduna ta ya bawa jami'an tsaro akan kokarin da sukai na kubutar da mutanen. Ya kara da cewa zuwa yanzu duk an sada mutanen da iyalansu. 


Aruwan ya Kara da cewa dakarun tsaro sun yi artabu da 'yan bindiga wanda hakan ya tilastawa 'yan bindiga tserewa cikin jeji domin tsira da rayuwar su. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post