Idan Saurayinki Ko Mijinki Na Cikin Fushi Dake, Yi Masa Wadannan Abubuwan Kiga Abin Mamaki


Babu soyayyar da ba a samun sabani a cikinta, sai idan soyayyar ta yaudara ce, kai ko ta yaudarar ce dole ne akan samu sabani. Domin duk inda za'a hadu to dole ne za'a samu sabani wasu lokutan. 


'Yan mata da matan aure suna da karancin sanin hanyoyin da za su rika tausasa manemansu da aure bayan sun bata musu rai. 


Shiyasa a wannan rubutun muka kawo muku wasu hanyoyin da za ku rinka shawo kan samarin ku Ko da kuma mazajen ku. A duk lokacin da kika samu matsala da masoyin ki, yi masa wadannan abubuwan a duk lokacin da kika bata masa rai.


1: Kada Ki Fushi Idan Saurayinki Na Fushi Dake.

2: Kada Ki Matsa Masa A Lokacin Bashi Iska.

3: Kada Ki Dauko Zancen Daya Haddasa Masa Fushin Idan Kina Bashi Hakuri.

4: Kada Kice Dole Nan Take Sai Ya Huce Ko Ya Hakura.

5: Ki Nuna Masa Rashin Kyautawarki Karara.

6: Ki Daurewa Ranki Dabi'unsa Na Wannan Lokacinda Yake Fushi Dake.

7: Kada Kiyi Saurin Shigo Da Wasu Zancen Naku.

8: Ki Fahimtar Dashi Irin Son Da Kike Masa Bana Muzguna Masa Bane 

9: Ki Nemi Taimakon Wani Na Kusa Dashi Idan Kin Kasa Shawo Kansa.

10: Kiyi Masa Alkawarin Bazaki Maimaita ba.

 

Duk namiji mai son mace na gaskiya dole ne zai rika samun matsala da ita irin na masoya. Sai dai kuma kada ku yawaita yin hakan domin zai shafi zaman aurenku nan gaba.


Abunda namiji yake so musamman idan yana da gaskiya a fushin da yake yi. Shi ne mace ta kaskantar da kanta wajen bashi hakuri da kuma nuna masa kaunarsa a ranta.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post