Matar shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wasu Hotuna na bikin murnar kammala karatun surukar su Zahra Bayaro wacce 'yar Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero ce.
Aisha a saman hotunan ta yi rubutu inda take taya murna ga surukar ta Zahra Bayero wacce ta kammala karatun Digiri na farko a fannin Zane-Zane wanda ta fita da matsayi mafi daraja na (first class).
A yayin da malaman jami'a ke cika wata bakwai suna yajin aiki amma kuma sai ga 'ya'yan shugabanni suna wallafa hotunan su na bikin kammala karatun su.