Wasu hotuna dake ta yawo a kafafen sada zumunta na fitaccen jarumi Umar Gombe da Hauwa Ayawa jaruma a cikin shirin Gidan Badamasi mai dogon zango.
Sai dai kuma wata majiya na bayyana cewa hotunan ba na auren gaske bane, na shirin Gidan Badamasi ne Kamar yadda shafin Film Magazine ya wallafa.
Film Magazine ta kara da cewa su wadannan hotunan an yi su ne domin shirin Gidan Badamasi da ake haskawa a tashar Arewa 24 wanda za'a dawo da haskawa a ranar 6 ga watan Oktoba na 2022.
Shi kansa darakta Falalu Dorayi da ya wallafa hotunan a shafin cewa yai, "Allah Ya sanya alkairi"
Umar Gombe & Hauwa AYawa
Komai yana da lokacin sa.
6 October, 2022
Don haka mutanen da suke yada labarin cewa Umar Gombe da Hauwa Ayawa za su yi aure ba gaskiya bane. Hotunan anyi su ne kawai don shirin Gidan Badamasi, Wannan ita ce gaskiyar lamari a kan hotunan.