Hoton 'yan matan Chibok uku da aka sake kubutarwa a hannun 'yan Boko Haram a ranar Juma'a


Rudunar Sojin Hadin Guiwa ta 'Operation Hadin Kai' ce ta yi nasarar kubutar da 'yan matan tare da 'ya'yansu a Jihar Borno.


A watan da ya gabata ma sojoji Sun kubutar da wasu daga cikin daliban makarantar sakandiren ta chibok a garin bama su 2 dauke da 'ya'yan su. 


A baya-bayan nan dai kungiyar 'yan tada kayar baya na Boko Haram da ISWAP suna fuskantar matsi daga wajen sojojin Najeriya inda ake yawan kai musu hare-hare a maboyar su wanda ke sanadin mutuwar su da kuma guduwa daga maboyar su. 


Dama dai gwamnatin Najeriya ta bada umarni ga rundunar tsaro da su yi gaggawar kawo karshen ayyukan 'yan ta'adda A fadin kasar kafin zuwa Karshen Disamba na 2022. 


Hoto: Hassan Ibrahim

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post