Harkar Film Ta Canja Min Rayuwa Domin Na Fara Samun Nasarori - Inji Amina A. Shehu


Sabuwar jaruma a masana'antar Kannywood Amina A. Shehu ta ce ta fara ganin nasarori tun bayan da ta shigo harkar finafinan Hausa. Inda tace ta fara ganin haske tun bayan da ta fara fitowa a finafinan. 


A wata tattaunawa da ta yi da mujallar film jarumar ta bayyana cewa ba ta da wani buri da ya wuce ta ga ta yi suna a harkar finafinan Hausa wanda tun tana yarinya take son shiga harkar finafinan. 


Amina 'yar asalin garin Zaria mai shekaru 23 ta shaidawa Mujallar Film cewa ta zo Kano gidan 'yan uwanta domin kawai take samu hanyar day za ta fatan shiga finafinan Hausa har kuma na yi nasarar samun shiga. 


Ta bayyana cewa tun a shekarar 2018 ne ta fara fitowa a finafinan hausa kuma zuwa yanzu ta fito a finfinai da dama irinsu Danja’, ‘Gidan Mato’ ‘Wata Makauniya’, da sauran su.”


Ta ce tana da burin ta kara samun daukaka har ta zama a cikin jerin fitattun Jarumai na gaba-gaba da ake yayin su. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post