Mata musamman sabbin amare ko kuma wadanda suke da burin haihuwa nan gaba ma'ana haihuwar farko. Yana da kyau ku fahimci wadannan abubuwan tun kafin cikin ya shiga domin kada ya zo muku da mamaki ko ban tsoro da fargaba.
Abubuwan suna da yawa sosai amma za mu kawo muku wadansu daga ciki masu muhimmanci, Wadannan abubuwan kuwa sun hada da:
1: Sauyin Jiki
2: Keda zuwa ganin likita kun kulla
3: Kada Ki Yawaita Matsala Da Mijinki
4: Zaki Daina Shan Taba Ko Giya (Ga mata masu sha).
5: Zaki Kauracewa Gurbatancen Muhalli Da Kuma Gujewa Waje Mai Doyi.
6: Zaki Rika Neman Shawarwari Wajen Wadanda Suka Taba Haihuwa.
7: Zaki Rage Cin Abincin Dake Saka Kina.
8: Kiyi Kokarin Neman Tarihin Gidanku Yadda Ciki Da Haihuwa Yake Zuwa Muku.
9: Zaki Daina Shiga wata Sabga Da Zai Jawo Miki Bacin Rai.
10: Za Ki Daina Sha'awar Cin Wasu Ci Maka.
Duk macen da take shirin daukan ciki yana da kyau ta san da cewa zata shiga wadannan har ma da wasu daba mu kawo ba a matsayin sabon rayuwar ta har sai bayan ta haihu.
A karshe muna addu'a masu neman Haihuwa Allah Ya basu. Wanda suke dasu Allah ya shirya su gabaki daya.