Dauda Kahutu Rarara Ya Bude Sabuwar Manhajar Kallon Finafinan Hausa Mai Suna Arewa Cinema - Android Pols - latest news, natural remedies, and entertainment

Dauda Kahutu Rarara Ya Bude Sabuwar Manhajar Kallon Finafinan Hausa Mai Suna Arewa Cinema


Dauda Abdullahi wanda aka fi sani da Rarara wanda fitaccen mawakin siyasa ne a Najeriya ya fito da wata manhaja wacce za'a iya kallon waƙoƙin Hausa da finafinan Hausa wacce a turance ake kira da streaming.


Rarara ya yiwa Manhajar suna da 'Arewa Cinema', kuma shi ne na uku irin sa da aka buÉ—e, wato bayan Northflix na Jamilu Abdussalam da kallo.com na Maijidda Modibbo.


Shafin 'Mujallar Film'  ta bayyana cewa mai taimaka wa Rarara a fagen soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya fada musu cewa lallai ubangidan nasa shi ne mamallakin manhajar ‘Arewa Cinema’, wanda hakan amsa ce ga masu tambayar wanene ya Æ™irÆ™iro ta kimanin mako biyu tun da aka fara tallata ta a soshiyal midiya.


A yanzu haka akwai finafinai da dama a kan manhajar, irin su ‘Mariya’, ‘Hafeez’, ‘Mujadala’, ‘Wutar Kara’, ‘Ana Dara Ga Dare’, ‘Salmah’, da sauran su. Akwai kuma finafinai masu dogon zango irin su ‘Wuff’ da sauran su, sannan akwai waÆ™oÆ™i na mawaka daban-daban.


Binciken mu ya gano cewa a tsarin biyan kuÉ—i kafin mutum ya fara kallo a manhajar, a shekara zai biya N9,500, sannan in duk wata ne zai riÆ™a biyan N1,000 ne. 


Sannan kuma mun gano cewa su ma masu ‘Arewa Cinema’ sayen fim su ke yi a hannun masu shiryawa kamar yadda sauran su ke yi. 


Sannu a hankali dai abubuwa na Æ™ara faÉ—aÉ—a a masana'antar  Kannywood, yanzu babban Æ™alubalen da ke gaban ‘yan Kannywood shi ne su ma a fara ganin finafinan su a Netflix.


Wannan manhajar ta 'Arewa Cinema' ta ja hankalin mutane sosai musamman masu ra'ayin kallon finafinan Hausa da waƙoƙin su.

Related Posts:
Previous article
Next article

Leave Comments

Post a Comment

Iklan Atas Artikel

Iklan Tengah Artikel 1

Iklan Tengah Artikel 2

Iklan Bawah Artikel