Labaran Kannywood
Dan Takarar Shugaban kasa A Jam'iyar APC Bola Tinubu Ya Gana Da 'Yan Kannywood
Friday, September 16, 2022
0
Dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu tare da mukarraban yakin neman zabensa sun tarbi tawagar masu shirya fina-finai Na Najeriya.
Jaruman shirya fina-finan sun hadar da na Kudu da kuma na Arewa wato Nollywood da Kannywood.
Minista Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ita ce ta jagoranci jaruman masana'antar shirya fina-finan a wajen wannan ganawa da aka yi dasu.
Yayin ganawa dasu Bola Ahmed Tinubu ya nemi hadin kansu domin zamowarsa sabon shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023.
Idan za a iya tunawa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya taba zama gwamnan jihar Lagos a shekarun baya.
Daga Suraj Na'iya Kududdufawa
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment