A wata hira da aka yi da shahararriyar jarumar finafinan Hausan nan da ta haska a zamanin baya kuma ta jagoranci samar da finafinai guda biyu Jan Ido da Bakar Tukunya, a wata hira da ta yi da jaridar Blueprint Fati Baffa wacce aka fi sani da Bararoji ta bayyana dalilan da ya sa har yanzu da take da shekaru sama da 30 ba ta yi aure ba.
Jarumar ta bayyana cewa tana yawan yin tafiye-tafiye ne zuwa kasashen ketare kamar su Saudi Arabia, Dubai da India domin gudanar da kasuwanci ta na saye da sayar da gwal da kayan ado, bayan na yi film din Jan Ido da Bakar Tukunya sai na ga ya dace na bar fim domin bada dama ga masu tasowa.
Da aka Kara tambayar Ko yanzu me take yi, ta ce da farko dai tana godewa masoyana da masu bibiyata, sannan kuma ina bukatar karin addu'arsu domin har yanzu ban yi aure ba kuma bani da, shekaru na sun haura 30 ni kuma Musulma ce budurwa.
Gaskiya abin na damun mahaifana da har yanzu ban yi aure ba, amma gaskiya a nan ita ce samun wanda za ka aura abu ne mai wahalar gaske, duk wanda zai zo wajenki sai ya rika ce maki ku rika haduwa a Otel, gidan saukar bakinsa, ko kuma wani wuri daban, wanda ni ban yarda da wannan ba, domin duk inda ka ga namiji da mace sun kebe to, na ukun su shaidan ne, ko da yaushe ina kauracewa wannan.
Wannan shi ya sa ko a gidan cin abinci na da wuya ma idan ka je ka ganni saboda bana zama sosai domin zamana a wajen zai ba wasu damar gayyata zuwa gurin daban, ina mamakin yadda wasu matan ke sayar da mutuncinsu ga wasu mazan.
An kuma yi mata tambaya akan soyayyar ta da wani Mawaki inda ta bayyana cewa dogon labari ne yana matukar sosa zuciyata, ba na son ana tada shi amma tunda ka yi wannan tambayar bara na fada maka, wannan mawaki sananne ne sunansa Abdu Boda dan Katsina ne.
Abdu Boda ya hadu matuka taren mu da shi tasa ya zama kamar daya daga cikin ahalin mu, yana zuwa gidan mu ko da bana nan sun shaku da kowa na gidan mu, kanwata ta kan yi masa girki su kuma yi hira sosai da 'yan gidan mu. Kowa ya dauka za mu yi aure, kwatsam sai wata kawata ta kirani ta ce mani ta ga katin daurin auren Abdu Boda da wata yarinyar bani ba.
Ina jin wannan mummunan labarin sai na yanke shawarar kiransa a waya kun san me ya faru? Ranar da na kira shi ranar ce daurin aurensa, amma sai ya rantse mani cewa abin da na ji ba gaskiya ba ne duk karya ce.
Labarai suka cika ko'ina na sake kiransa ya kara karyata zan ce sai nayi sauri na shirya na dauki shatar mota zuwa Katsina sai na iske ana ta shagalin biki na halarci liyafar cin abincin biki na dawo gida, amman fa haryanzu ina jin sonsa a zuciyata.
An sake tambayar ta kan yadda take jure wannan lamarin, sai ta bayyana cewa Shiryawa na yi na tafi umara na roki Allah sosai akan ya cire lamarin a zuciyata na kuma ci gaba da addu'a ba dare ba rana daga nan na samu sauki.
An kuma tambayar ta kan cewa Ya ki ke ji yanzu ganin cewa ba ki yi aure ba? Ta bayyana cewa duk lokacin da na halarci wani taron harkar fim na kan ga 'yan mata matasa bakin fuska wannan shi ya sa na kara fita daga harkar fim, amma duk lokacin da na je na iske kawayena irinsu Sadiya Gyale, Rukayya Dawaiya, Saima Muhammad, Rashida Adamu da Asma'u Sani na kan ji dadi kuma na kan ji kamar in dawo fim.
Daga karshe an tambaye ta mai za ta ce a kan harkokin ki da suka hana ki harkar fim? Inda ta bayyana cewa, ban san amsar da zan ba ka ba, amma bara na baka wani dan misali, kamar dan siyasa ne ya fadawa karuwa yana so ta yarda da shi bai taba yin karya ba, bai taba cin amana ba saboda shigarsa ta kamala, a nata jawabin ita kuma sai ta ce masa tun da take karuwancinta ba ta taba saduwa da wani da namiji ba, ita ma ya gaskata ta sai su yi aure to, kamar haka ne ni ma kasuwancina bai hana ni fim ba ina fatan ka fahimta.
Daga Anas Abubakar Dan Aunai