Usman Abubakar Rimi, dalibin Jami'a ne dake a shekarar karshe a fannin likitanci da tiyata a Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, UDUS, ya koma sayar da abinci a kan titi sakamakon yajin aikinda malaman jami’o’in ke yi, da yaki ci ya ki cinye wa.
A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, a ranar Juma’a a Sokoto, Abubakar-Rimi ya ce ya dauki wannan matakin ne domin su samu abin yi, duba da yadda yajin aikin ya tilastawa dalibai zaman kashe wando.
Abubakar-Rimi, wanda ya mallaki wajen sayar da abinci da Indomie a cikin birnin Sakkwato, ya bayyana cewa yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i, ASUU ke ci gaba da yi ne ya ba shi cikakkiyar dama.
Ya bayyana cewa ya tsunduma cikin harkar siyar da abinci a cikin watanni biyun da suka gabata, inda ya bayyana sana’ar a matsayin mai riba.
“Na karbi hayar shago, na kuma dauki ma’aikata guda takwas masu dafa min shayi da hada-hadar indomie, ina sayar da lemuka da ruwan sha na kwalba da gwangwani, masa, shinkafa da wake, miya da nama tare da kasuwancin POS.
“Ana sayar da farantin abinci daga N200 zuwa sama, iya karfin aljihun mutum ” in ji Abubakar-Rimi.
Ya bayyana cewa ya mallaki wani shago a titin Fodio, shima a cikin babban birnin Sokoto, inda yake sayar da kayan sawa na maza da mata, hula, jakankunan makaranta da takalmi.
“A ko yaushe ina farin cikin ganin cewa na zama mai samar da aiki, kamar yadda a halin yanzu na dauki mutane 10 a cikin shagunan biyu.
Ya kara da cewa “Na dogara da shagunan wajen samun kudin shiga masu kyau, saboda ba na tambayar iyayena kudi duk da cewa an rufe makarantu.”
Dalibin ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya samo bakin zaren warware yajin aikin da ke cigaba da gudana domin amfanin matasa da kuma ci gaban kasa.
Ya kuma yi kira ga malaman jami’o’i da su yi la’akari da halin da daliban ke ciki tare da warware matsalar.
Ya kuma roki ASUU da su amince da wasu tayin da gwamnatin tarayya ke yi domin illar yajin aikin ya yi kamari a kan kowane bangare na 'yan Najeriya.
A baya-bayan nan dai ana yawan samun dalibai suna komawa yin sana'a domin su dogara da kansu duba da yadda yajin aikin ASUU yaki karewa tsawon watanni takwas da aka shafe ana yi.