Malam Umar Sani Jigirya wanda ake yiwa lakabi da Sallau a cikin shirinnan mai farin jini na "Dadin Kowa" wanda gidan talabijin na Arewa 24 suke yi, ya bayyana cewa tun bayan da aka daina saka shi a cikin shirin na "Dadin Kowa" ya koma harkokin sa inda yake aiki a gidan Radio.
Rashin ganin Sallau a cikin shirin na "Dadin Kowa" yasa mutane suka dinga tambaya Ko mai yasa ba'a ganin sa. Wasu na tambayar lafiyarsa, wasu kuwa na neman sanin dalilin da yasa aka daina saka shi a cikin shirin.
Hakan yasa wata kafar Jarida ta "Film Magazine" ta samu ta tattauna da jarumin akan dalilan da yasa aka daina ganin sa a cikin shirin na Dadin Kowa wanda ya bayyana musu cewa babu wata rashin lafiya Ko makamancin hakan da yasa aka daina saka shi.
Ya ce, shirin ‘Daɗin Kowa’ ba ni na samar da shi ba, na wasu ne da su ka samar da masu rubutun labari su ka rubuta masu, su ke ɗaukar ma’aikata kuma ni ma sai ya zama ina cikin wanda labarin ya kira ni, su ka ga na dace da shi su ka ɗauke ni a daidai lokacin da labarin ya kira ni.
“Domin ai ka ga a farkon shirin ‘Daɗin Kowa’ babu Sallau, sai daga baya Sallau ya shigo, kuma ana tafiya Sallau ya je gaɓar da babu shi. Kusan sau biyu ko uku Sallau ya na tafiya ya na dawowa.
“To, wannan yanayi ne na labarin da su masu rubutun za su duba su ga a ina mutum ya dace ya fito, a ina ya dace a ajiye shi. Wani ma za ka ga kashe shi ake yi a labarin. To, duk yanayi ne ya ke zuwa da haka, don haka ko da an ga a yanzu babu Sallau a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’, to labarin ne ya zo da haka.
“Ta yiwu kuma nan gaba labarin ya dawo da Sallau ko kuma ya tafi kenan.”
Dangane da ko a ina ya sa gaba a yanzu kuwa, sai jarumin ya ce, “To da man ni ina aikin jarida, don na yi aiki a gidan Rediyon Rahama, sannan na yi aiki a gidan Rediyon Arewa, sannan kuma kusan shekara talatin ni ɗan fim ne da na fara tun ana wasan daɓe.
“Don haka a yanzu ina yin harkokin da su ka shafi rediyo da fim da tallace-tallace. Kai, har ma siyasa ina yi tun a lokacin baya! Don haka ba na tsaya ba ne ina yawon maula.