An hallaka 'yan bindiga fiye da 40 a yayin wani luguden wuta da sojin saman Najeriya suka dajin Zamfara da Katsina


Akalla 'yan bindiga su 43 ne suka mutu a yayin wani hari da rundunar Sojin saman Najeriya suka kai musu a maboyar su dake jihar Zamfara da Katsina. 


An kai harin ne a dajin Birnin Magajiya, Jibia da kuma Zurmi da sauran maboyar 'yan bindigar da ba'a bayyana ba. A yayin harin dai an kashe da dama daga cikin cikin 'yan bindigar ciki har da Dogo Rabe wannan babban yaron Bello Turji ne. 


Harin da rundunar Sojin saman suka kai na zuwa ne kwanaki hudu da suka kai wani hari ga maboyar fitaccen dan ta'addan da ya addabi jihohin Zamfara da Katsina Bello Turji wanda aka kashe yaransa fiye da ashirin sai dai shi Bello Turji ya tsere. 


Abdulbaqi Aliyu wani dan jarida ne dake jihar Zamfara, ya shaidawa jaridar Premium Times cewa 'yan bindiga da suka mutu sun haura su 40 a yankin Birnin Magajiya. 


Rundunar Sojin saman Najeriya ta ce hare-haren dakarunta a dajin sabon birnin dan Ali cikin karamar hukumar Birnin Magaji ya kashe ‘yan ta’adda 40, batagarin da wata majiya ke cewa suke aikata satar shanu a yankin.


Wani mazaunin garin Abdullahi Mamman Zurmi ya tabbatar da cewa a yayin harin an kashe  Gwaska Dankarami wanda jagoran yan bindiga ne a yankin na Zurmi. 


Yace yawan 'yan bindigar da aka kashe zai iya haura 40 domin yayin kai farmakin 'yan bindigar suna gudanar da taro a wani gida karkashin jagorancin Dankarami lokacin da Sojin Najeriya suka jefa bom a cikin gidan wanda ya tashi dasu gabaki daya. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post