An Gano Gawarwaki Mutum 15 Cikin Wani Kogi A Maiduguri Sakamakon Amabaliyar Ruwa


Sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka a wasu sassan jihohin Najeriya wanda hakan ya jawo ambaliyar ruwa a gurare da dama sakamakon hakan ne mutane da dam suka rasa rayukansu da gidajen su. 


Wani rahoto dake fitowa daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na cewa akalla gawarwakin mutum 15 ne aka tsinta a kogin Ngadabul da ke birnin, bayan wami mamakon ruwan sama da ya jawo ambaliya.


Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) na shiyyar Arewa maso Gabas, Muhammad Usman, ne ya tabbatar da alkaluman a ranar Laraba a wata tattaunawa  da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Maiduguri.


Ya ce, mutanen da suka nitse a cikin kogin wadanda ke gabarsa ne kuma adadin zai iya karuwa idan an gama gudanar da bincike. Sannan kuma ya gargadi iyaye da masu kula da su da su fadakar da ‘ya’yansu ke zuwa yin ninkaya a cikin kogin don guje wa nitsewa a ciki.


Haka kuma yace ambaliyar ruwa a yankin Arewa maso Gabas na da matukar tayar da hankali, duba da rashin magudanar ruwa masu inganci da rashin gyaran kwalbati. 


“NEMA a matsayinta na hukumar ba da agaji ta tsunduma aikin wayar da kan jama’a kan illolin ambaliya da matakan kariya daga ita domin jama'a su kare kansu daga fadawa halaka. 


“Muna ta ganawa da masu ruwa da tsaki daban-daban kan wayar da kan jama’a da kuma samar da kayan agaji ga al’ummomin da abin ya shafa,” cewar Usman.


A halin da ake ciki kuma, tuni rundunar tsaron farin kaya ta sibil defens (NSCDC) reshen Jihar Borno ta tura jami’anta gabar kogin domin fatattakar yaran da ke shirin shiga ciki da nufin yin ninkaya.


Tun a makon da ya gabata dai an samu ambaliyar ruwa a sassan jihohin arewacin Najeriya wanda hakan ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. Ko a ruwan da aka yi a ranar Litinin a jihar Kano sai da ya haddasa ambaliya a wasu daga cikin manyan kasuwannin garin. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post