Kwanan nan ne aka tsinci gawar dalibai uku na Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu (COOU), Igbariam Campus a masaukin su a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba.
Rahotanni sun bayyana cewa, daliban da suka rasu sun hada da Obidiaso Chidera, dalibi mai digiri matakin 200 a fannin kimiyyar siyasa, Mercy, dalibar sanin magani, da Emmanuella, dalibar harkokin kasuwanci, an tsinci gawarsu a dakin kwanan dalibai na Goodluck da ke jihar Anambra.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, an gano gawar daliban uku ne bayan wasu daliban da ba su gansu ba sun je masaukin domin yin tambayoyi. Kwankwasa kofar da aka yi na tsawon lokaci ba'a amsa ba, don haka daliban suka yanke shawarar karya kofar da karfi bayan sun gano gawarwaki biyu marasa rai a kan gadajen dakin yayin da aka tsinci gawar ta uku a cikin kicin.
Hukumar makarantar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta tabbatar da faruwar lamarin sai dai ta bayyana kaduwar cewa har yanzu wasu daliban na nan a gidajen kwanansu duk da cewa an rufe makarantar a watan Agusta. Hukumomin makarantar sun ce jami’an tsaro na gudanar da bincike a kan lamarin kuma za a bayyana sakamakon zaben.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LIB, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya ce;
''Tun daga lokacin aka fara bincike kuma an gano gawarwakin. Mun kuma gano wasu abubuwan da ake zargin na muggan kwayoyi ne kuma jami’an binciken mu sun mamaye wurin da lamarin ya faru kamar yadda Kwamishinan ya bayar da umarnin mika karar zuwa ga SCID domin gudanar da cikakken bincike”.