Abubuwan Da Marigayiya Ummita Ta Fadamin Akan Saurayinta Dan China Kwanaki 7 Kafin Rasuwarta - Inji Sheikh Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa fitaccen malamin addini a jihar Kano ya bayyana abubuwan da Ummita ta fadamasa kwanaki bakwai kafini rasuwarta.
Shehin Malamin a wani faifan bidiyo da ya fitar na karatunsa ya bayyana irin abubuwan da Ummita ta fadamasa akan saurayinta dan China a wayar tarho da yai da ita.
Malamin ya bayyana yadda hirar su ta kasance da Ummita inda yace ta kira shi don neman shawara kan mafita game da auren dan China wanda iyayenta basa son auren.
Inda na bayyana mata cewa iyayenta sun yi gaskiya akan hana ta kin auren dan China wanda ba jinsinta bane kuma ake kokonto akan asalin sa ba, cewar malamin.
Sai dai malamin ya ce ya bata shawarar ta gindaya wa masoyin na ta sharÉ—É—a biyar kafin su yi auren.
“Sharadi na farko shi ne a tuntubi hukumar shige da fice ta Æ™asa don tabbatar da ko da izini ya shigo Æ™asar nan. Na biyu, a yi bincike kan aikin sa a Najeriya.
“Na uku, na san Sarkin Kano ya naÉ—a sarkin Æ´an China a Kano. Don haka a tambayi shugaban al'ummar kasar ko sun san shi, yankin da ya fito da kuma abin da yake yi?
“Na huÉ—u, ya kamata kuma a sanar da ofishin jakadancin cewa É—an kasar China na shirin auren Æ´ar Najeriya. Na biyar kuma na umarce ta da ta sanar da Hisbah don ta kara koya masa addinin musulunci, tunda ta ce min ya musulunta.
“Ummita ta kara da cewa iyayensa a kasar China sun amince da auren, amma iyayenta sun ki amincewa da auren.
"Amma na gaya mata idan kun cika waÉ—annan sharuÉ—É—a guda biyar, zan shawo kan iyayenki su yarda ki aure shi," in ji shi.
Daurawa ya ƙara da cewa addinin Musulunci ya amince da auren jinsi, yana mai cewa addinin ya kyamaci nuna wariyar launin fata, inda ya ƙara da cewa marigayiyar ta faɗa masa cewa ɗan China ɗin ya musulunta.
Sheikh Daurawa ya kuma yi kira ga hukumomin da su ke da ruwa da tsaki da su tabbatar an hukunta É—an China da ya kashe Ummita.
Mutumin mai suna Gheng Quanrong ne ya hallaka Ummita, bayan da ya caccaka mata wuƙa a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano.
Leave Comments
Post a Comment