Breaking News
Yan bindiga sun sace matan aure 3 da budurwa 1 a wani sabon hari da suka kai a Katsina
Sunday, August 7, 2022
0
'Yan bindiga sun sace matan aure 3 da budurwa 1 a wani sabon hari da suka kai a Katsina
'Yan ta'adda sun yi garkuwa da mata guda hudu a karamar hukumar safana ta jihar katsina.
A daren ranar asabar wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kutsa kai cikin garin Safana dauke da makamai.
Jaridar Katsina post ta rawaito cewa a yayin kai harin ne dai maharan suka yi garkuwa da mata guda 4 Suka tafi da su zuwa maboyar su cikin jeji.
Matan da suka dauka din guda 3 Matan aure ne sai budurwa guda daya. Har kawo yanzu dai babu wani cikakken bayani game da inda suke.
A baya-bayan nan dai hare-haren 'yan bindiga a Jihar Katsina sai karuwa yake, wanda kuma haryanzu mahukunta ba su dauki wasu mataki na kawo karshen lamarin ba.
Previous article
Next article
Leave Comments
Post a Comment