Tarihi: Jihar Jigawa ta cika shekaru 31 da kafuwa a matsayin jiha


Jigawa na daya daga cikin jihohi 36 dake Nigeria, tana cikin yankin Arewaci, wacce kafin kafuwar ta suna hade ne da Jihar Kano sai kuma daga baya aka cire ta daga tsohuwar jihar Kano a shekarar 1991. 


Sannan kuma jihar ta Jigawa ta yi iyaka da wasu yanki na kasar Niger kamar su Babura, da sauran su. Dutse shine ne babban birnin jihar ta Jigawa. 


Jihar Jigawa tanada Ƙananan hukumomi guda ashirin da bakwai (27) da suka hada da:


- Auyo

- Babura

- Biriniwa

- Birnin Kudu

- Buji

- Dutse

- Gagarawa

- Garki

- Gumel

- Guri

- Gwaram

- Gwiwa

- Hadejia

- Jahun

- Kafin Hausa

- Kaugama

- Kazaure

- Kiri Kasama

- Kiyawa

- Maigatari

- Malam Madori

- Miga

- Ringim

- Roni

- Sule Tankarkar

- Taura

- Yankwashi


Akwai masarautun gargajiya guda biyar a wannan jiha ta Jigawa da suka hada da: 


- Masarautar Dutse

- Masarautar Kazaure

- Masarautar Hadejia

- Masarautar Ringim

- Masarautar Gumel


Daga lokacin da aka ƙirƙir wannan jiha ta Jigawa zuwa yau (2022), ta yi gwamnoni guda takwas, ga Sunayensu kamar haka:


- Manjo Janar Olayinka Sule


- Barr. Ali Sa'adu


- Brigadier General Ibrahim Aliyu


- Colonel Rasheed Alade Shekoni


- Colonel Abubakar Zakariyya Maimalari


- Alhaji Ibrahim Saminu Turaki


- Alhaji Sule Lamiɗo


- Alhaji Mohammad Badaru Abubakar, mon, mni


Ko wanene sabon gwamnan Jigawa a shekarar 2023? Allah masani !! 


Abubakar Lecturer ✍️

 

27/8/2022

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post