Malam ya ce a binciken da ya gudanar mafi akasarin matan da ke saka sarka a kafafun su a yammacin duniya mata ne karuwai ko matan auren da ke mu'amala da wasu mazan ko kuma 'yan madigo.
Amma duk matan kirki ba za su saka sarkar kafa ba, don haka musulmi ya guji wannan. Matan mu masu rawar kai wajen yin ado da sarkar kafa su yi gaggawar dainawa.
Saka sarka a kafa dai za'a iya cewa sabon abu ne musamman a kasar Hausa wanda a shekarun baya ba'a saba ganin irin hakan ba, sai dai kuma a wannan lokacin ana ganin wasu daga cikin matan Hausawa suna saka sarka a kafafun su domin yin ado.
Amma dai Sheikh Usman ya gargadi mata akan su daina saka sarka a kafafun su domin ba ala'dar mutanen arewa bane kuma ba koyarwar Musulunci bane.