Ambaliyar ruwa ta haifar da asarar dukiya ta biliyoyin nairori a kasuwar Kantin Kwari
Ruwan saman da aka kwashe sama da awanni hudu ana yinsa a birnin Kano ya jawo asarar dukiyoyin yan kasuwa a kantin kwari.
Wasu daga cikin 'Yan kasuwar da ambaliyar ta shafa sun koka game da toshe magudanan ruwa a sakamakon aikin gadar sama da ake yi da wasu gine-gine da ake gudanarwa a kasuwar.
Wani fitatacen Dan kasuwar a kantin kwari Mujitapha Tanko Danbaba, ya shaidawa gidan Radio na Express cewa tun da aka kafa kasuwar ba'a taba shiga irin wannan haliba.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta duba hallin da kasuwar take ciki duba da yadda ambaliyar ruwan ta shafi masu karamin karfi.
Wakiilin Radio Express Kano Nazifi Bala Dukawa, ya tuntubi Manajen Daraktan kasuwar Kantin Kwari, Abba Muhammad Bello, inda yace zai yi bayanin halin da ake ciki Amma har zuwa wannan lokaci bai bayyana musu komai ba.
Leave Comments
Post a Comment