Yanzu-Yanzu: Kotun Koli ta Sake Tabbatar da Hukuncin Kisa ga Jarumar Kannywood


A rana irin ta yau 8 Ga Watan Yuli 2011 Kotun Ƙoli ta tabbatarwa jarumar Kannywood kisa ta hanyar rataya.


Rabi Isma'il Yar Asalin Kabilar Auchi ce Daga Jihar Edo ce Amma Haifaffiyar Tudun Wada A Kano, Ta Fito A Fina-finan Kannywood Wanda Su ka Hada Da Tsumagiya,  Da Aya, Da Manakisa.


A Ranar Kirsimetin Shekarar 2002, Rabi Ta Tunkuda Saurayinta Alhaji Ibrahim Zazu Cikin Ruwan Tiga, Inda Rai Yayi Halinsa. Amma Kafin Ta Tunkudashi Shi Cikin Ruwan, Saida Ta Bashi Alewa Chocolate Din Ekiles Wacce Tayiwa Cushe Da Maganin Bacci, Saida Rabi Ta Tabbatar Ya Fita A Hayyacinsa Sannan Ta Lalube Aljihunsa Ta Kwashe Kudi Naira Dubu Dari, Kana Ta Tunkudashi Cikin Ruwan.


Wannan Dama Ya Nuna Da Niyyar Kisa Ta Tura Auwalu Zazu Cikin Ruwa. Jami'an Binkice Sun Gano Rabi Ta Aikata Hakane Domin Ta Gaje Dukiyarsa. Kasancewarsa Hamshakin Maikudi.


Don Haka A Ranar Janairun Shekarar 2005 Babbar Kotun Jihar Kano Ta Sameta Da Laifin Kisan Kai. Mai Shari'a Halliru Muhammad  Abdullahi Ya Yanke Mata Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya, Saidai Rabi Ta Daukaka Kara A Kotun Daukaka kara Da ke Kaduna. A nanma Dai Kotun Ta Tabbatar wa Da Rabi Laifinta. Daga Nan Kuma Sai Kotun Koli Da ke Abuja. Inda A Rana Mai Kamar Ta Yau Ne 8 Ga Watan Yuli 2011 Kotun Ta Tabbatar Mata Da Kisa Ta Hanyar Rataya. 


Alkalin Kutun Guda Bakwai Karkashin Mai Shari'a Francis fiddodi Tabai, Sunce Sun Gamsu Da Hujjujin Da Aka Bayar A Kotun Farko Don Haka Suka Tabbatar Mata Da Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya. Sai Dai Kamar A Fim! A Ranar 16 Ga Watan Disambar 2011, Sai Rabi Isma'il Tayi Batan Dabo Daga Gidan Yarin Hadeja Inda Aka Neme Ta Aka Rasa.


Bayanai Sunce A Kurkukun Kano Aka Daureta Inda Daga Baya A ka Mayar Da Kurkukun Kaduna Lokacin Da Ta Daukaka Kara. In da A Can Ne Kuma Ta Zama Jan Wuya, Inda Ta Rika Safarar Sigari Da Kwaya Da Wiwi. Harma Anyi Zargin Rabi Tana Sharholiyarta Ne Da Manyan Jami'an Fursun A Lokacin Da Ta ke A Tsaren. 


Bayan Da Kotun Koli Ta Yanke Mata Hukuncin Kisa Sai Aka Sauya Mata Matsuguni Zuwa Hadeja. A Hadejanne ta Yaudari Wani Babban Ganduroba Inda Suka Tsunduma Cikin Kogin Soyayya. Ana Wannan Halinne Ta ke Shaida Masa Cewa Ta Mallaki Miliyoyin Naira, Kuma Da Zai Nema Mata Bizar Amurka Ya Fitar Da Ita Daga Kurkuku Zata Aure Shi," Su Tare A Can Suyi Ta Cin Duniyarsu Da Tsinke. Haka kuwa A kai A Ranar 16 Disambar 2011, Sai Jami'in Nan Yayi Hanyar Da Rabi Ta bi Ta Sulale Daga Kurkukun Nan.


Sai Dai A Ranar 21 Ga Watan Mayun 2017,  Jami'an Tsaro Na DSS Su ka Cafke Rabi Isma'il A Kan Iyakar Najeriya Da Jamhuriyyar Benin, Daga Nan Su ka mika Ga Hukumar Kula Da Gudajen Kurkuku Ta Kasa A Inda Suka Sa ma Mata Gurbi A Gidan Kurkukun Kuje Da ke Abuja. Shi kuma Ganduroban Da Ya Taimaka Mata An Rage Masa Mukami Tare Da Sauya Masa Wajen Aiki. Haka Dai Baiwa Abokan Aikinsa Da Yawa Dadi Ba! Kasancewar Laifinsa Ya Cancanci kora Da Gurfana A Gaban Kotu.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post