'Yan bindiga sun kai hari kan ‘yan kungiyar Ansaru a karamar hukumar Birnin-Gwari ta Kaduna inda suka kashe mutane


Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ‘yan kungiyar suna tsaka da yin wa’azi ga jama’ar yankin ne a lokacin da ‘yan bindiga suka bude wuta, inda suka kashe mutanen kauyen biyu. 


An ce ‘yan bindigar sun kai farmakin ne a kauyen Damari da ke karkashin gundumar Kazage a Gabashin karamar hukumar a kokarinsu na fatattakar ‘yan ta’addan daga kauyen. 


Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan ta’addan suka mamaye al’umomin Gabashin karamar hukumar, inda suke jagorantar mutanen kauyukan kan hare-haren ‘yan bindiga. 


Ishaq Usman Kafai, shugaban kungiyar cigaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce an dauki tsawon sa’a guda ana arangama tsakanin kungiyoyin biyu. 


A cewarsa, ‘yan kungiyar ta Ansaru wadanda su ma dauke da muggan makamai sun yi galaba a kan ‘yan bindigar wanda hakan ya sanya su (’yan bindiga) suka koma kauyen. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post