Wani mutum da har yanzu ba a bayyana sunan sa ba, kuma mazaunin Lekki Face One, a unguwar Eyenkorin a Ilorin babban birnin jihar Kwara ya kona gidan sa kurmus.
Mummunan lamarin, a cewar mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hakeem Adekunle, ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:28 na safiyar Lahadi.
Ya ce, wani Mista Kola da ke zaune a unguwar, shi ne ya yi gaggawar kiran hukumar kashe gobara, domin sanar da su tashin gobarar.
Jami’an kashe gobara ya kuma ce, sun kashe gobarar a kan lokaci tare da hana ta tashi zuwa wasu gine-gine.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa, mutumin ya ce: “Da gangan ya watsa man fetur a dakunan na sa guda uku, sannan ya banka wuta saboda takaicin matarsa.”
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Prince Falade John Olumuyiwa, ya bukaci jama’a da su kara sanya ido a gidajen su ko ofisoshin su.